
Tun daga ranar da Amina ta kalle shi da murmushi na farko, Isma’il ya fara jin wani sabon yanayi a ransa.
Ba soyayya kawai ba ce. Wani irin tsoro ne mai dadi.
Sun fara gaisawa a hankali. Farko “Sannu.” Sai ya koma “Yaya karatu?” Daga baya ya zama tattaunawa mai ɗaukar lokaci.
Amina ba ta da yawan magana, amma idan ta fara, kalamanta suna shiga zuciya kai tsaye. Tana da buri, tana da mafarki, tana son rayuwa mai cike da mutunci da kwanciyar hankali.
Isma’il ya fara ganin kansa a cikin mafarkinta.
Rana daya suna zaune a harabar makaranta bayan an tashi. Iska mai sanyi na kadawa. Amina ta ce masa:
“Isma’il… ka taba jin tsoron rasa mutum?”
Ya yi shiru na dan lokaci.
“Eh,” ya amsa a hankali. “Amma ban taba jin tsoron rasa wanda bai zama nawa ba.”
Ta yi murmushi, amma murmushin ba cikakke ba ne. Kamar wanda ke boye wani abu.
Wannan rana ta fara canza komai.
A CIKIN SOYAYYA NA BACE Episode 1
Isma’il ya fara jin kamar akwai wani sirri a zuciyarta. Wani abu da take kokarin ɓoyewa. Wani abu da zai iya rushe komai.
Amma soyayya ta riga ta fara kama shi.
Ya fara saba jin muryarta kafin barci. Ya fara fara’a idan ya ganta. Ya fara jin zuciyarsa na tafiya inda take.
Bai lura ba… yana bacewa a ciki.
Bai lura ba… yana daina zama shi kansa.
Kuma bai san cewa ba shi kadai bane a zuciyarta ba.
